Jami’an tsaro a Chadi sun yi amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla wanda ake kira tiyagas a turance domin tarwatsa ɗaliban wasu makarantu kwaleji biyu da ke zanga-zana a N’Djamena babban birnin ƙasar.
Ɗaliban sun fito ne suna zanga-zangar ƙin jinin Faransa da safiyar Litinin kamar yadda jaridar Tchad Infos ta ruwaito.
Sun fito zmaan titi suna yayata cewa “Faransa ta fie daga Chadi, a cewar jaridar.
Wannan na zuwa bayan masu masu fafutika sun jagoranci zanga-zangar kyamar Faransa a garin Ati na Chadi.