Shugaban hafsun sojojin kasa, Taoreed Lagbaja, ya amince da sababbin nadi da kuma wasu sauye-sauyen manyan jami’ai a fadin Najeriya.
Darektan hulda da jama’a na sojojin kasa, Onyema Nwachukwu ya sanar da wannan a wani jawabi. The Cable ta fitar da rahoto a yammacin Asabar.
Janar Lagbaja ya umarci wadanda su ka samu mukamai su kara kokarin wajen yakar kalubalen da ake fuskanta na ta’addanci da tada zaune-tsaye.
Jawabin Onyema Nwachukwu yace, nadin mukaman da aka yi sun kunshi:
1. AB Ibrahim — Sashen dabaru da tsare-tsare (DAPP)
2. BR Sinjen — Sashen ayyukan sojoji (DAOPs)
3. OR Aiyenigba — Sashen auna ayyukan sojoji
4. NC Ugbo — Sashen hulda da farar hula
5. E Akerejola — Sashen kai da komawa a Hedikwata
6. BA Alabi — GOC na Hedikwata ta I
7. AE Abubakar — GOC na Hedikwata ta 3/Kwamandan Operation Safe Haven (OPSH)
8. PP Mala — GOC na Hedikwata ta 7/Kwamandan bangaren dakarun Operation Hadin Kai (OPHK).
9. GU Chibuisi — Kwamandan bangaren dakarun Operation Hadin Kai (OPHK).
10. IS Ali — Kwamandan rundunar hadin gwiwa MNJTF
11. EAP Undiandeye — Shubaban leken asiri (NIA)
12. OO Oluyede — Kwamandan Sojojin yaki
13. MG Kangye — Kwamandan Sojojin da ke rike bindigogi
14. AA Adeyinka — Kwamadan sufuri a Hedikwata
15. KO Aligbe — Kwamdan horaswa
16. JO Ochai — Kwamandan makarantar NDA
17. IB Maina — Kwamandan makarantar ilmin yaki
18. TB Ugiagbe — Shugaban sashen leken asirin sojoji
19. OG Onubogu — Kwamandan cibiyar Martin Luther Agwai
20. N Ashinze — Darekta a sashen DIA
21. AO Onasanya — Shugaban sojojin fadar shugaban kasa