yammacin jiya ne, masu aiki ceto 82 na kasar Sin da aka tura zuwa Turkiya don gudanar da aikin ceto, suka dawo gida kasar Sin. Ma’aikatan tawagar ceto daga yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ma suna daga cikin wadanda suka dawo gida ta cikin jirgin saman.
Bayan da ma’aikatan tawagogin ceto na Sin suka isa yankin da bala’in girgizar kasa ya shafa a kasar Turkiyya a ranar 8 ga watan Faburairu, bisa yankunan da bangaren Turkiya ya tabbatar, sun je lardin Hatay, wato daya daga cikin yankunan da bala’in girgizar kasa ya fi shafawa don gudanar da aikin ceto.
A lokacin da ake aikin ceto, kasar Sin ta tura tawagogin ceto har guda 21, da suka kunshi ma’aikata 308. Wadannan ma’aikatan Sin sun ceto mutane 6 da zakulo gawarwaki 11 daga baraguzan gine-gine a lokacin da suke tantance da kuma yin aikin ceto a cikin gine-gine 87, da suka kai fiye da murabba’in mita dubu 700.
Yayin aikin, tawagogin Sin sun tinkari matsaloli iri iri kamar kananan bala’un girgizar kasa da tsananin sanyi da karancin kayayyaki da cunkoso da sauransu, sun yi aikin ceto tukuru tare da himma da kwazo.
Aikin ceto da tawagogin Sin suka yi, ya sami yabo matuka daga bangaren Turkiya. A yayin bikin ban kwana da tawagogin ceto na kasar Sin da gwamnatin Turkiya ta shirya, Mr. Ismail wanda ke kula da aikin daidaita harkokin shiyya-shiyya a ma’aikatar harkokin waje ta Turkiyya ya bayyana godiya sosai ga aikin tawagogin ceto na Sin. Ya ce, kokarin da tawagogin ceto na Sin suka yi, zai inganta ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.