Babu mu babu zaben kowacce jam’iya har sai an magance mana matsalolin mazabar mu— Alummar Sharada

An bukaci mahukunta da su rika jajircewa kai da fata  da yin duk mai yuwuwa wajen ganin sun sauke nauyin dake wuyan su na al’umma.

Bukatar hakan ta fito ne ta bakin al’ummar unguwar Sharada a lokacin da suke tsaka David gudanar da Zanga-zangar lumana da matasan unguwar suka jagoranta kan matsalar da ta dabaibaye su ta rashin samun Hasken wutar lantarki har na tsawon watan fiye da hudu.

A cewar Wani mai suna Tanimu tunda randar rarraba wutar unguwar ta su ta sami matsala aka dauke ta hanyar yanzu ba’a dawo da ita ba kuma basu sami wata a madadin ta ba

Ya kara da cewa sun bibiyi mahukunta akan batun amma har kawo yanzu ba su samu an dawo musu da taransifomar ta su ba ko kuma samun wata a madadin wadda aka dauke da sunan gyara.

Yace yanzu basu da abin da za su iya face su fada wa yan siyasar da suke Son kuri’un su cewar Baza suyi zabe ba har sai an magance musu wannan matsalar ta su.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments