Putin ya bijiro da dokar da zata tabbatar da yankuna hudu da ya mamaye a Ukraine karkashin ikon sa

RelatedPosts

A jawabin da ya sanar na sanya dokar ta bacin, Putin ya ce mayakan sa-kai masu akida irin ta Hitler na kokarin kafa kungiyar ‘yan sari ka noke, tare da tura baradensu don shirya wa Rasha makarkashiya, dalilin da ya tilasta musu daukar wannan mataki a kokarin kakkabe barazanar.

Putin ya bayyana cewa mahukuntan Ukraine ne suka tsara harin da ya karya gadar kerch da ke yankin Crimea, baya ga kitsa wasu jerin hare-haren ta’addanci a yankuna da dama na Rasha ciki har da wuraren da fararen hula ke rayuwa, da cibiyoyin da ke jigilar makamashi har ma da na nulkiliya duk dai a yunkurin karya Moscow amma kuma jami’ansu suka yi nasarar dakile hare-haren.

Shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa tun gabanin hadewar yankunan 4 da suka kunshi jamhuriyar Donesk, da jamhuriyar Louhansk, da Kherson da kuma Zaporoziya tuni suka kasance karkashin dokar ta baci, saboda haka abin da za a yi a yanzu shi ne tabbatar da su a karkashin dokar, wanda a cewarsa ta haka ne za a kawo karshen barazanar ‘yan ta’addan.

Putin ya ce tuni ya rattaba hannu kan kuduri doka wanda ya mikawa kwamitin tsaro na tarayya domin neman amincewarsa game da shirin.

RelatedPosts

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments
Kasar Amurka ta amince da Kara rura wutar rashin zaman lafiya tsakanin Isra’ila da abokan adawarta

Kasar Amurka ta amince da Kara rura wutar rashin zaman lafiya tsakanin Isra’ila da abokan adawarta

Wani jami'in Amurka ya tabbatar wa kafar yada labarai ta BBC cewa ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta sanar wa majalisar ...

Sojojin Cameroon sun fuskanci mummunan hari daga Yanbindiga

Sojojin Cameroon sun fuskanci mummunan hari daga Yanbindiga

Jami'ai sun ce ƴanbindiga sun kashe sojojin Kamaru aƙalla shida a wani hari da suka kai kan iyakar ƙasashen biyu. ...

Jawabin shugaban kasar Sin, Xi Jinping na sabuwar shekarar 2025

Jawabin shugaban kasar Sin, Xi Jinping na sabuwar shekarar 2025

’Yan uwa da abokai, maza da mata, barka dai. Lokaci na gudu cikin sauri, kuma sabuwar shekara na gabatowa. Ina ...

Kasar Ivory coast ta bi sahun Niger ta yanke alaka da Faransa

Kasar Ivory coast ta bi sahun Niger ta yanke alaka da Faransa

Sannu-sannu dai Faransa na ci gaba da rasa tasirin da take da shi a wannan yanki na Afirka ta Yamma, ...