Wasu kungiyoyin mata sama da ashirin a Jihar Adamawa sun yi zanga-zangar lumana domin nuna goyon bayansu ga Senata Aishatu Dahiru Ahmed Binani wadda kotu ta rushe nasarar zaben fidda gwani da ta samu a kwanakin baya.
Hukuncin, wanda aka yanke ranar Juma’a, a kotu karkashin jagorancin Mai Shari’a A.M. Anka ta ce zaben anyi shi ba bisa ka’ida, saboda haka Senata Aishatu Dahiru Ahmed Binani ta daina gabatar da kanta a matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa ta jam’iyyar APC.
Kungiyoyin Mata Sun Yi Zanga-zangar Goyon Bayan Aishatu Dahiru ‘Yar Takarar Gwamna A Jihar Adamawa
Comfort Ibrahim Ezira shugabar kungiyar mata ‘yan siyasa a Jihar Adamawa, wadda kuma ita ce ta jagoranci zanga-zangar, ta bayyana cewa su mata suna bukatar adalci akan wannan shari’a da babbar kotun gwamnatin tarayya ta yanke.
Madam Duni Musa Jambutu da ta wakilci mata ‘yan kasuwa a Zanga-zangar tace ba su ji dadin wannan al’amari ba. Ta na mai bayyana cewa an nuna wa mata bambancin jinsi da kuma danniya a siyasance.
Shi kuwa Mustafa Salihu Mataimakin Shugaban jam’iyyar ta APC Shiyarar Arewa Maso Gabashin Najeriya ya ce a bangaren jam’iyyar ba za su bar al’amarin ya tafi a haka ba suna kokarin daidaitawa,