Osinbajo yayi kakkausan martani akan makudan kudaden da ake baiwa hafsoshin tsaro

Mataimakin Shugaban kasa  Yemi Osinbajo ya bukaci sojojin kasar da su yi wa jama’a bayani akan irin makudan kudaden da gwamnati ta basu domin gudanar da ayyukan tsaro a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Osinbajo ya ce jama’ar kasa na da hurumin sanin irin makudan kudaden da wannan gwamnati ta ware domin tinkarar matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya wanda ke kaiwa ga rasa dubban rayuka, dan kore shakku dangane da yadda gwamnati ke fuskantar kalubalen tsaro.

Mataimakin shugaban kasar ya ce abin takaici ne kowanne lokaci idan anyi maganar tsaro, sai kaji wasu sojojin na cewa basu da kayan aiki, saboda haka ya dace ma’aikatar tsaro ta gabatar da wani tsari wanda zai dinga bayyana irin kudaden da su ke kashewa a bangaren tsaro.

Osinbajo ya bayyana cewar ya dace ace Najeriya ta shawo kan matsalar ‘yan bindigar da ake fama da ita ta wajen nuna kwarewa da kuma nuna dabarun yaki.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta gabatar da kasafin kudin tsaron da aka baiwa ma’aikatar tsaro tun shigowar gwamnatin Buhari a shekarar 2015 kamar haka:

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments