Al’umma da jami’an lafiya a Kudancin Sudan sun ce kimanin mutum 15 ne aka kashe bayan sabanin da aka samu kan fili a jihar Blue Nile.
Rikicin ya samo asali ne sakamakon ce-ce-ku-ce tsakanin al’ummar Hausawa da kuma wasu kungiyoyin adawa da ke wani karamin gari, mai tazarar kilomita 500 kudu da babban birnin kasar, Khartoum.
Mazauna yankin sun bayyana cewa sun ji karar bindiga sannan an cinna wa gidaje wuta.
Ma’aikatan asibitin da ke garin sun ce an kai musu gawarwakin mutane.
Rikicin ya barke ne duk da tsauraran matakan tsaro a yankin wanda aka kafa dokar hana fitar dare sakamakon rikicin fili a makon da ya gabata inda aka kashe mutane da dama.