Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi rantsuwa a shari’ar ɓata sunan da wata mata E. Jean Carroll da ya musanta yi mata fyade ta shigar a kansa.
A tsakiyar shekarun 1990 lokacin ta yi wannan zargi. Sai dai Donald Trump ya mayar da martani ne yana matsayin shugaban Amurka da cewa bai taɓa haduwa da ita ba kuma ba ajinsa ba ce sannan karyata take.
Mista Trump ya dade yana ta fafutukar neman kotu ta dage shari’ar amma a makon da ya gabata ne alkali ya ki amincewa da bukatarsa.
Lauyar Trump ta ce wannan ma wata makarkashiya ce da ake yi wa wanda take karewa.