Guda daga yan majalisar gudanarwa na kasar China kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana ta kafar bidiyo da Csaba Korosi, shugaban babban zauren MDD na 77, a jiya Litinin.
Ya bayyana yadda a ko da yaushe kasar Sin ke goyon bayan muradun MDD da muhimmiyar rawar da babban zauren majalisar ke takawa, Wang Yi ya ce, Sin za ta ci gaba da shiga ana damawa da ita a hadin gwiwar kasa da kasa kan sauyin yanayi, tare da bayar da gagarumar gudunmuwa ga nasarar taro karo na 27 na bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta COP27 da ma yarjejeniyar kare muhalli domin tunkarar sauyin yanayi ta MDD wato UNFCCC.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta shirya yin musaya da hadin gwiwa kan albarkatun ruwa da sauran kasashe ta hanyar aiwatar da Shirin Raya Duniya na Global Initiative.
A nasa bangare, Csaba Korosi, ya taya Sin murnar gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20, kana ya bayyana fatan karfafa hadin gwiwa da kasar wajen cimma nasarar taron COP27 da kuma taimakawa kasashe masu rauni shawo kan kalubalen da suke fuskanta wajen amfani da kuma tsimin ruwa. (