Mijina Ba Ya Kula Da Ni, Na Gaji, Wata Mata Ta Nemi Kotun Shari’a Ta Raba Aurensu

Wata matar aure mahaifiyar mutum huɗu, Kafayat Yusuf, a ranar Laraba ta maka mijinta, Abdulwahab Yusuf, a gaban Kotun shari’ar Musulunci dake zama a Magajin Gari, Kaduna. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Matar ta nemi Kotun ta raba auren saboda Maigidanta ba ya kula da ita ko kaɗan kuma babu wani tallafi daga ‘yan uwansa.

Kafayat ta shaida wa Kotu cewa Yusuf ya watsar da ita da ‘ya’yan da Allah ya azurtasu da samu tsawon watanni 9 ba tare da ya waiwayi halin da suke ciki ba.

A ɓangaren magindanci wanda bai halarci zaman Kotun ba, lauyansa Malam Abdulbasit Sulaiman, ya bayyana cewa ya nemi wanda yake karewa ta wayar salula amma bai same shi ba. Sai dai Lauyan ya roki Kotu da ta ba shi wani lokaci domin ya tuntubi wanda ake tuhuma don su tattauna kan lamarin. Bayan sauraron haka, Alkalin Kotun mai sharia Malam Rilwanu Kyaudai, ya sanar da ɗaga sauraron ƙarar har zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba, 2022.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments