Hukumomi a Iran sun ce aƙalla mutum 15 ne suka mutu a loƙacin da aka kai hari wani wurin bauta da ke kudancin kasar.
Kafar yaɗa labaran Iran ta rawaito cewa wasu mutum 19 sun ji mummunan rauni lokacin da aka bude wuta kan masu ibada a yammacin Laraba a wurin bauta na Shah Cheragh da ke yankin Shiraz.
Cikin hotunan da kafar talbijin ɗin ta nuna, an ga yadda jini yake malala ta kasan ginin, yayin da mutane ke ta gudu, wasu da rauni, wasu na kokarin taimakon wadanda suka fadi.
Shugaba Ebrahim Raisi ya dora alhakin harin kan masu tsaurin kishin Islama mabiya Sunna.
Ƙungiyar ISIS mai iƙirarin jihadi ta ɗauki alhakin kai harin.