Napoli na tattaunawa kan dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, sai dai daraktan kulub din na Italiya Cristiano Giuntoli ya yanke shawara kan dan wasan na Portugal. (DAZN, via Talksport)
Liverpool ne kulub na baya-bayan nan da yake zawarcin dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes, sai dai su na fuskantar takara da kungiyon Chelsea da Real Madrid, matukar Newcastle United za ta iya shawo kan dan wasan mai shekara 24 ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da su. (TNT Sports – in Portuguese)
Chelsea na neman dan wasan baya na Inter Milan da Netherlands Denzel Dumfries, mai shekara 26, a kokarin da ta ke yi na neman dan wasan da zai maye gurbin dan wasanta da ya ji rauni wato Reece James, mai shekara 22. (90 Min)
Shugaban kungiyar Inter Milan Steven Zhang ya ce mai tsaron gidan Slovakia Milan Skriniar, wanda a kai amanna kungiyar Paris St-Germain, ta sanyawa kahon zuka kuma ba za ta taba bari a yi cinikinsa ba, shugaban ya ce ya yi amanna dan wasan mai shekara 27 zai ci gaba da kasancewa a kulub din serie A. (Sky Sport Italia, via Football Italia)
Tottenham ka iya sakarwa dan wasan Sifaniya winger Bryan Gil, mai shekara 21, mara da mai tsaron gida na Ingila Japhet Tanganga, dan shekara 23, da su bar kungiyar nan da watan Janairu mai zuwa, ya yin da ta ke zawarcin dan wasan baya na dai Ingilar Djed Spence, dan shekara 22. (Times – subscription required)
Juventus na duba yiwuwar daukar dan wasan Ingila Winger Samuel Iling-Junior mai shekara 19 kan sabuwar yarjejeniya, in da bangarorin biyu za su ci gaba da tattaunawa kan batun da suka fara da dadewa. (Calciomercato – in Italian)
Arsenal ta tattauna kan sabon kwantiragin daukar darakta Edu, wanda yake aiki da wata kungiya a Tarayyar Turai. (Evening Standard)
Everton na nuna ra’ayin daukar dan wasan gaba na Portugal Daniel Podence, wanda ake sa ran kwantiraginsa da Wolves ya kai kakar 2024. (Football Insider)
Nottingham Forest na Shirin kashe tsakanin fam miliyan 50 zuwa 100 a watan Janairu, domin bude kofar yin musayar ‘yan wasa, da karfafa gwiwar yiwuwar ci gaba da kasancewar ‘yan wasan a Premier League. (Football Insider)
Ana fatan Barcelona za ta rattaba hannu kan maye gurbin dan wasan tsakiya na Sifaniya Sergio Busquets mai shekara 34, nan da watan Janairun badi. (ESPN)
Kungiyar Manchester City ta rattaba hannu kan dan wasan tsakiya Emilio Lawrence mai shekara 17 daga Everton. (Fabr izio Romano)