Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tayi bayanin abin da ya sa ta gaza sauya ‘dan takarar sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar NNPP Malam Ibrahim Shekarau.
Premium Times ta rahoto hukumar INEC tana cewa ba zai yiwu a maye gurbin Malam Ibrahim Shekarau da wani ‘dan takara, duk da ya canza sheka ba.
Shugaban sashen shari’a na INEC na reshen jihar Kano, Suleiman Tahir ya shaidawa manema labarai cewa sabuwar dokar zabe ba ta bada damar canjin ba.
Da yake bayani a makon nan, Malam Suleiman Tahir ya nuna INEC ba ta san da maganar janye takarar tsohon gwamnan ba, domin ba a sanar da ita ba.
Sabuwar dokar zabe ta shekarar 2022 ba ta bada dama a cire sunan ‘dan takara haka kurum ba, sai idan ya rubuto takardar janye takararsa ko kuma ya mutu.
“Sabuwar dokar tace da zarar an sa sunanka da farko, kafin a fitar da sunayen karshe na ‘yan takara, mai takara zai rubutawa INEC, ya hada da hotonsa.