Wasu daga cikin jami’an gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun yi Allah wadai da kalaman Firaministan Mali Abdoulaye Maiga, wanda ya cacaki wasu kasashen Afirka cikinsu har da shugaba Bazoum Mohammed.
Maiga wanda ke jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zargi Faransa da goyawa ‘Yan ta’adda baya, yayin da ya yi zargin cewar shugaban Nijar Bazoum Mohammed ba ‘dan kasa bane.
Ministan Harkokin Wajen Nijar Youssouf Mohammed Elmouctar ya yi mummunar suka akan kalaman Firaministan, wanda ya ce babu dalilin yin su ko kadan.
Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Nijar Mohammed Saghdoun ya bayyana Maiga a matsayin sojan da bai fahimci yadda al’amura suke ba a kasarsa.
sanarwar da ya raba wa manema labarai, dan majalisar ya soki irin matakan da sojin Mali suke dauka wadanda suka kasa kare lafiyar fararen hular kasarsu, abind da ya tilasta wa adadi mai yawa na fararen hula barin kasar domin samun mafaka a Nijar tun daga shekarar 2012.
Saghdoun ya bukaci Nijar ta kira jakadanta da ke Mali domin ya koma gida tare da katse huldar diflomasiya da gwamnatin kasar wadda ya ce take yi wa Rasha aiki.
Ya zuwa wannan lokaci, gwamnatin Nijar a hukumance ba ta ce komai ba dangane da kalaman Firaministan Malin