Kwamitin Majalisar Dattawa mai Kula da harkokin ‘yan sanda ya saurari bahasin Jama’a akan wani kudurin doka da zai bada dama a kafa hukumar kula da fansho na ‘yansanda.
Sanata Elisha Abbo wanda ya kawo kudurin ya ce yana so Majalisa ta amince da shi cikin ‘yan watannin nan da su ka rage kafin karshen wa’adin majalisar.
A taron sauraron bahasin da Kwamitin kula da harkokin ‘yan sanda na Majalisar dattawa ya shirya, kudurori biyu ne aka ji ra’ayoyin jama’a akan su da na kafa Hukumar Fansho na ‘Yan sanda wanda Sanata daga Adamawa ta Arewa Elisha Abbo ya kawo, sai na kafa cibiyar horar da ‘yan sanda na musamman wanda Sanata Mai wakiltan Borno ta Kudu Mohammed Ali Ndume ya kawo.
Masu ruwa da tsaki da dama ciki har da tsofaffin ‘yan sanda da suka yi ritaya sun nuna goyon bayan su ga kudurorin musamman ma na kafa Hukumar Fansho.
Kamar yadda Abubakar Dashe tsohon dan sanda mai ritaya ya yi tsokaci.
Dashe ya ce ya ajiye aiki a shekara 2007 kuma yana da anini uku a lokacin, amma ya zuwa yanzu Hukumar pansho na tarayya wato PENCOM ta na biyan shi Naira dubu 30 ne a wata.
Dashe ya ce yana ganin wannan mataki da majalisar dattawa ta ke son dauka zai yi tasiri domin zai ba tsofaffin ‘yan sanda dama na cin moriyar sadaukar da rayukansu da suka yi tun suna raye.
Sanata Mai wakiltan Adamawa ta arewa Elisha Abbo ya ce ‘yan sanda sun canci kulawa ta musamman.
Abbo ya ce aikin ‘yan sanda aiki ne na sadaukar da rai, kuma mai wuya, saboda haka yana ganin lokaci ya yi da za a ba ‘yan sanda kula ta musamman domin su samu karfin gwiwar gudanar da aikin su.
Shi kuwa, shugaban Kwamitin Kula da Harkokin ‘yan sanda a majalisar dattawa Dauda Halliru Jika, ya bada tabbacin yin aiki akan kudurorin domin ganin an cimma burin kawo su.
Jika ya ce kwamitin sa zai gabatar wa Majalisar Dattawa da rahoton irin bayanan da aka yi a lokacin sauraren bahasin tare da tabbatar da kudurorin biyu sun samu karbuwa kamar yadda masu ruwa da tsakin suka nema.
Sufeto Janar na ‘yan sanda Alkali Baba wanda Mataimakin Sufeto Sanusi Lemu ya wakilta, ya nuna goyon bayan sa ga kudurorin musamman ma na kafa Hukumar Fansho.