Kungiyar matuka Akori kura ta kasa reshen jihar Kano dake railway ta koka kan yadda yayanta ke fuskantar kalubale sakamakon dokar mayar da tsoffin kudade bankuna kafin nan da karshen watan nan.
Shugaban kungiyar na kasa reshen railway da ke nan kano Alhaji Dan Iya Bala ne ya yi wannan koken a zantawarta da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Dan Iya Bala ya bayyana cewar wannan tsarin ya samarwa da yayanta matsaloli kasancewar suna daukar kayayyaki daga nan kano zuwa sassa daban daban na kasarnan Wanda har ta sanya a wasu jihohin kudancin kasarnan bama sa karbar tsoffin kudade.
Don haka Shugaban ya umarci yayan kungiyar su kan cewar duk wanda bashi da asusun ajiya banki ya tabbatar ya mallakeshi.
Shugaban ya kuma bayyana cewar idan har gwamnati tace zata yi wani abu to lallai yana da muhimmanci don haka yake kira ga yayan kungiyarsu kan cewar su zauna cikin shiri Wato duk wanda yasan asusun ajiyarsa na banki na da matsala yaje ya gyara nan da kafin lokacin rufe karbar tsoffin kudade da babban bankin kasarnan ya sanya.
Dan Iya Bala ya kuma yi Kira ga gwamnatin tarayya kan ta daure ta kara waadin lokacin daina yin amfani da tsoffin kudaden da ta sanya kasancewar alummar kasarnan musamman mazauna karkara na kokawa kan cewar tsarin zai haifar wa da tsarin kasuwacinsu barazana sakamakon mafi akasarin su basu da asusun ajiyar banki.
Daga karshe Shugaban kungiyar ya shawarci yan kungiyarsu kan su kasance masu bin doka da oda a dukkan lamuran su kuma su rungumi dukkan wani tsari da gwamnati ta bijiro dashi don cigaban kasa da bunkasar tattalin arzikin kasuwanci da sanaoi a fadin kasarnan.