,Shugabancin ma,aikatar kasuwanci da masaaantu ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa bijiro da managartan tsare tsare
da Zasu bunkasa kasuwanci da tattalin arzikin jihar nan.
Kwamishinan ma,aikatar kasuwanci da masanaantu na jihar Kano Batista Ibrahim Mukhtar ne ya yi wannan yabon a taron manema labarai na karshen shekara daya gudana a ofishinsa dake nan kano.
Batistan ya bayyana cewar babban kalubalen da ya addabi kasuwanci bama a kasarnan ba har ma da duniya baki daya shi ne cutar corona wadda ta dakatar da kasuwanci a duniya ta kuma durkusar da tattalin arzikin kasashe wanda har yanzu wasu kasashen ba su gama farfadowa ba.
Sai kuma kalubale na kwanan nan Wato yakin kasar rasha da kasar Ukraine wanda yayi Sanadiyar hauhawar farashin kayayyaki a kasuwannin duniya ciki har da kasashe masu tasowa.
Saga nan kuma sai Matsalar tsaro wanda shi kuma yayi tasiri sosai a kasashe kamar irin su Najeriya.
Sai dai kuma ya yabawa gwamnatin Dakta Abdullahi umar Ganguje khadimul Islam bisa rawar da ya taka wajen bunkasa kasuwanci da cinikayya musamman ma a bangaren tsaro yayi kokari wajen Sanya naurorin daukar hoto da bayanai a Manyan dazukan jihar Wato Dajin falgore da Dajin dan soshiya ta yadda batagari da yan bindiga ba Zasu samu damar kafa sansani a dazukan ba.
Kazalika ya bayyana cewar wannan ya yi fafutikar ganin an bude kasuwar tsandauri ta Dala Dry port ta yadda yan kasuwa a jihar Kano Zasu iya fitarwa da kuma shigowa da kayayyakinsu ba sai sun dogara da tashar ruwa da ke ikko ba wanda an kammala ta kuma ana sa ran Shugaban kasa mujammadu Buhari zai kaddamar da ita a farkon shekara mai kamata.
Kwamishinan baya ga irin wadannan nasarori da aka samu a bangaren kasuwanci ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar Kano ta kuma gina kasuwar duniya wadda babu irin ta a duk fadin nahiyar Afrika ta yamma wanda komai an tanadar masa da wajensa kuma an yi shi cikin tsari ta yadda ko daga ina Kazo zaka iya cin kasuwar cikin kwanciyar hankali ka kuma koma inda ka fito lafiya.
Kazalika ya kuma bayyana cewar gwamnan ya kuma bude Manyan kasuwannin hada hadar wayoyin hannu a jihar wadda mafi akasarin masu sanaar matasa ne wanda hakan ya taimaka wajen Samar musu da aikin yi ta yadda zasu dogara da kansu a fadin jihar Kano.
Ya kuma kara da cewa sakamakon tsaro da jihar Kano take dashi ya sanya yan kasuwa daga jihohi daban daban na kasarnan suke zuwa suke bude kamfanonin casar shinkafa wanda babu Wata jiha a kasarnan da ke fitar da yawan shinkafar da ake fitarwa a jihar nan.
Daga karshe Kwamishinan yayi fatan alheri ga daukacin alummar jiharnan tare da fatan samun karuwar arziki mai dorewa.
From Shehu Suleiman Sharfadi