Wata kotu a birnin Accra ta tasa keyar wasu yan Najeriya hudu zuwa gidan Yari, kan laifukan hada baki tare da sace wasu mata yan kasar Canada biyu a shekarar 2019.
An sami yan Najeriyan da laifin garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa da ya kai dalar Amurka dubu 800, har ma da yin barazar aikata fyade.
Masu shigar da kara kotu sun tuhumi matasan biyu da suka hada da Elvis Ojiyorme da Yusif Yakubu kan laifukan hada baki da kuma garkuwa don kudin fansa, har ma da barazanar yin fyade ga matan idan ba a ba su kudin fansa ba, wanda hakan ya sa kotu ta yanke musu hukuncin daurin shekaru goma a gidan Yari.
Bincike jami’an tsaron kasar Ghana ya kai ga kamo mutanen da ake zargin a jihar Ashanti.
Amina Muhammad yar fafutukar kare hakkin mata a Ghana, ta jinjina wa mahukunta bisa wannan matakin kamawa tare da ladabtar da wadanda suka aikata laifin, lamarin dake kawar da fargaba ga masu niyyar zuwa Ghana yawon bude ido.
Shi ma Musah Akambonga, mai sharhi kan harkokan tsaro ya bai wa gwamnati shawara kan matakan kare yan kasashen waje, don kare sake faruwar hakan nan gaba; tare da jan hankalin mahukunta da suka kara dagewa don gyara lamarin tsaron Iyakokin kasar.
A baya-bayan nan Ghana ta fuskanci matsalolin tsaro musamman na garkuwa da mutane a wasu yankuna da suka hada da Jahar Ashanti da jahar tsakiya, tare da jahar yamma abin da ma shugaban majalisar tsaron jahar Ashanti Hon Simon Osei Mensah ya fada wa manema labaru a gefen taron atisayen soja domin dakile duk wani yunkurin ta’addanci a Ghana, cewa hukumomi na aiki tukuru domin dakile duk wani abin da ke barazana ga tsaron kasar.