Lokaci yayi da matasa zasu gane girman da suke da shi: kungiyar matasan yan kasuwar Gama

Shugabancin kungiyar matasan yankasuwar unguwar gama gidan kara ya shawarci matasan jihar kano, musamman na yankin gama,da su kaucewa shiga bangar siyasa a wannan lokaci na siyasa da ake ciki,musamman yadda zabe yake karatowa.

Shugaban matasan yankasuwar Alh.mustapha Abubakar ne ya tabbatar da haka a zantawarsa da manema labarai a nan jihar kano.

RelatedPosts

Yace, lokaci ya yi da matasa ya kamata su yi karatun ta nutsu wajen kaucewa duk abin da zai haifar da fitina cikin alumma da kin yarda a yi amfani da su domin tayar da rigima ko wasu abubuwa da za su kawo tsaiko tafiyar da alamuran siyasa.

Mustapha Abubakar, ya kuma yi kira ga matasa da su kaucewa shan muggun kwayoyi da sauran kayayyakin maye da yawo da makamai da za su kai ga illata lafiyar alumma ko furgitasu.

Shugaban ya kuma ce,ta fannin kasuwanci a kasar nan, ya zama koma baya mutika Wanda alamura sun lalace,tattalin arzikin kasuwanci ya karye Wanda yana bukatar yin duba na tsanaki domin farfado da shi yadda ya kamata.

Shugaban ya bukaci Gwamanatoci a matakai daban daban, da su kasance masu sanya yankasuwa a cikin tsarin kasuwanci da suka bijiro da shi domin bunkasar harkakin kasuwanci, maimakon dakko mutanen da basu San kasuwanci ba.

Yace, idon Gwamanatin tana yin irin wannan tsari to yankasuwa da dama za su amfana da abubuwa da yawa da kuma,sharbar roman damakaradiyya ta yadda za su bunkasa kasuwancinsu da Samarwa matasa sana,oin dogaro da kai Dan rage talauci da zaman kashe wando da rashin ayyukan yi a ci alumma.

Ibrahim sani gama pyramid radio.

RelatedPosts

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest