Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya ce bai goyi bayan dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi karara ba a zaben da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu domin babu wanda ya tattauna da shi kan takarar Igbo.
Sakataren yada labarai na kungiyar kabilar igbo, Ohaneze Ndigbo, na Dr Alex Ogbonnia ne ya bayyana hakan a Enugu inda yace Wike ya bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar ta yi da shi a Fatakwal a jiya Alhamis.
Ogbonnia ya bayyana cewa, a wajen taron, Ohaneze Ndigbo ta fuskanci Wike a kan zargin da ya yi wa Obi a lokacin zaben shugaban kasa.
Ya ce Wike ya bayyana mamakin da yadda Ohanaeze ke kokarin gano gaskiya kuma zai bayyana irin rawar da ya taka a zaben shugaban kasa.
A cewar Ogbonnia, gwamnan Rivers ya bayyana cewa kungiyar gwamnonin kudu sun fara ganawa ne a Asaba inda su ka amince cewa mulki ya koma Kudu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya kuma bayyana cewa daga baya gwamnonin sun hadu a Enugu a watan Satumba na 2021 don tabbatar da matsayinsu na komawa Kudu.