Manchester United na shirin sayen dan wasan Napoli Victor Osimhen, dan Najeriya mai shekara 23, yayin kungiyar ta Old Trafford ke neman dan gaba mai kai hari a kaka ta gaba.(Manchester Evening News)
Sai dai kuma kungiyar na fuskantar gogayya daga Real Madrid, inda Carlo Ancelotti ke kokarin shawo kan shugaban zakarun na Sifaniya Florentino Perez ya dauko Osimhen, da kuma dan AC Milan da Portugal Rafael Leao, a watan Janairu. (Sport via Mail)
Haka kuma Manchester United din na son sayen matashin dan wasan tsakiya na Benfica Enzo Fernandez, dan Argentina mai shekara 21. (Record via Mail)
Liverpool kuwa tana sha’awar matashin dan wasan Borussia Dortmund ne Youssoufa Moukoko, dan Jamus mai shekara 17, wanda ya ci kwallo shida a wasa 13 a bana. (Bild via Sporting Witness).
Hankalin Bayern Munich bai kwanta ba kan sayen dan gaban Tottenham Harry Kane duk da rahotannin da aka yi ta yadawa a watan da ya gabata da ke nuna cewa dan Ingilar shi ne na farko da kungiyar ta Jamus ke so. (Bild, via The Sun)
Dan wasan tsakiya na Uruguay Facundo Pellistri, mai shekara 20, yana son barin Manchester United gaba daya bayan da ya gama zaman aro a Alaves ta Sifaniya. (Mail)
Antonio Conte na sa ran ci gaba da zama a Tottenham, kuma zai kulla sabon kwantiragi da kungiyar ta London in ji mataimakinsa Cristian Stellini. (Evening Standard)
Arsenal za ta yarda ta biya farashin da Shakhtar Donetsk ta sanya na fan miliyan 56 a kan dan wasanta na gaba na gefe Mykhaylo Mudryk, dan Ukraine kasancewar Gunners din na gaba-gaba a kungiyoyin da ke son matashin mai shekara 21. (Give Me Sport)
Sabon kociyan Wolves Julen Lopetegui na sha’awar dauko ‘yan wasan Real Madrid Nacho Fernandez, dan Sifaniya da kuma Mariano Diaz dan Dominica. (Goal)
Chelsea na sha’awar sayen dan bayan Atletico Madrid Jose Maria Gimenez, dan Uruguayan. (SportWitness)
Masu kungiyar Newcastle United za su kashe karin fan miliyan 70 a cefanen ‘yan wasa a bazaran nan domin ci gaba da yi wa kungiyar garambawul. (Sun)
Kungiyar na harin sayen dan wasan tsakiya na Borussia Monchengladbach Kouadio ‘Manu’ Kone, dan Faransa a watan Janairu. (Bild – in German)
Nan gaba kadan Newcastle din kuma za ta gabatar da tayin matashin dan wasan tsakiya na kungiyar Velez Sarsfield dan Argentinian Maximo Perrone mai shekara 19. (Express)
Kazalika Newcastle din na sha’awar dan gaban Real Betis Nabil Fekir, dan Faransa inda ake cewa cinikin zai kai kusan yuro miliyan 50. (Mundo Deportivo)