Chelsea na duba yiwuwar sayen dan wasa a bazara mai zuwa inda dan wasan Napoli kuma mai bugawa Najeriya, Victor Osimhen mai shekara 23 ya zama zabi na farko yayin da suke duba wasu damarmakin. (90 Min)
Dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham, 19, ya zama dan wasan da Chelsea take hange yayin da mai bugawa Ingila kuma dan wasan West Ham Declan Rice mai shekara 23, shi ma hankali ke kansa. (Evening Standard)
Arsenal za ta fafata da Barcelona da Real Madrid wajen kulla yarjejeniya da dan wasa Endrick mai shekara 16 wanda aka yi wa lakabi da magajin Pele. (FourFourTwo)
Kocin Manchester United Erik ten Hag yana jan kafa wajen yanke shawara kan makomar mai tsaron ragar Spaniya David de Gea mai shekara 31 da dan wasan Ingila Marcus Rashford dan shekara 24. (Guar dian)
Dan wasan PSV Eindhoven Cody Gakpo, 23, ya ce yunkurin komawa Manchester United bai tabbata ba inda Leeds United da Southampton suma ke sha’awar sayen dan wasan mai bugawa Netherlands kafin ya yanke shawarar zama a kungiyarsa. (Times – subscription required)
Barcelona na bibiyar halin da dan wasan Manchester United mai shekara 23, Diogo Dalot, da kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa amma akwai damar a tsawaita ta zuwa shekara daya. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Daraktan kwallon kafa na Manchester United John Murtough ya soke duk wani fata na cinikin ‘yan kwallo a Janairu in da ya jaddada cewa kungiyar na dakon kasuwar musayar ‘yan kwallo ta bazara mai zuwa. (Telegraph – subscription require d)
Wakilin Dan wasan Portugal Ruben Neves ya yi wa dan wasan tsakiya na Wolves tayin zuwa Barcelona da ke yin nazari kan dan shekara 25 din. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Dan wasan Wolves Adama Traore, 26, ya ce yana fatan wata rana zai koma buga kwallo a Spaniya. (AS – in Spanish)
Kocin Kungiyar kwallon kafa ta Ingila Gareth Southgate zai bibiyi dan wasan Liverpool Joe Gomez mai shekara 25 kafin ya fitar da jerin tawagar da za su buga gasar cin kofin duniya a watan Nuwamba. (Times – subscription required)
Dan wasan Manchester United Michael Carrick, 41, a shirye yake a nada shi a matsayin sabon kocin Middlesbrough bayan da ya amince da sharuddan kungiyar. (Mail)
Kocin Crystal Palace Patrick Vieira ya ce kungiyar na cikin tattaunawa kan tsawaita kwantiragin dan wasan gaba na Ivory Coast Wilfred Zaha mai shekara 29 duk da alakarsa da Arsenal da Chelsea inda kuma kwantiraginsa ke shirin karewa a bazara mai zuwa. ( Metro)