Matar Shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta ce saboda yawan burin da ‘yan Najeriya suka ci a kan gwamnatinsu, ba ta da tabbas ko sun biya wa ‘yan ƙasar buƙatun nasu.
Aisha ta bayyana hakan ne cikin wata hira ta musamman da BBC cikin harshen Ingilishi, tana mai cewa wannan dalili ne ya sa ta nemi afuwar ‘yan ƙasar.
Rahotanni sun ambato ta tana bai wa ‘yan Najeriya haƙuri game da wahalhalun rayuwa da suke fuskanta yayin addu’o’i na musamman da ta shirya a ranar 1 ga watan Oktoba don bikin cika shekara 62 da samun ‘yancin-kan ƙasa.
A farkon watan Oktoban ne jam’iyyarsu ta APC mai mulkin ƙasar ta naɗa Aisha Buhari a matsayin jagorar tawagar kamfe ta mata a matakin takarar shugaban ƙasa.
“Burikan da aka ɗora mana suna da matuƙar yawa. Mutane sun ɗora burika a kanmu, kuma wataƙila bayan shekara bakwai ba mu cika musu dukkan burikan ba.
“Allah ne kaɗai ya san abin da ke zuciyar mutane. A matsayinka na ɗan Adam, ba za ka iya cewa ka yi daidai ba, ko kuma ka ce ka yi abin da ya kamata. Saboda haka gwamnatin ta yi ƙoƙari, amma ba lallai haka kowa ke gani ba.
“A wajensu sun yi ƙoƙari, Allah kaɗai ya sani. Saboda haka dole mu bai wa ‘yan Najeriya haƙuri ko da mun cika musu burinsu ko ba mu cika ba.
Ina gudanar da ofishina tamkar ƙungiyar agaji ne; kawai ina karɓar mutane ne amma ba na harkar siyasa. Abinda nake yi kawai shi ne mara musu baya ta ɓangaren lafiya
“Munsan za’a dinga tina mulkin mu da yiwa Al’umma hidima Muna bai wa yara kayan makaranta. Mun aro wasu abubuwa daga ƙudirorin jam’iyya kuma muka yi amfani da su wajen yaƙin neman zaɓe; bai wa yara abinci ta yadda hakan zai ba su ƙarfin gwiwar zuwa makaranta.
“Mun fuskanci babban ƙalubale saboda lokacin da mijina ya hau mulki ba kuɗaɗe, amma na dage a kan cewa mu ne muka ce za mu yi kuma dole ne mu yi.
Na gode wa Allah da ya ba ni damar zama matar shugaban ƙasa. Babban matsayi ne. Na gode wa Allah kuma ina roƙonsa ya sa mu gama lafiya, mu sake miƙa wa gwamnatin APC mulki.
“shugabar matan nigeriyar tace Ba ni da wani buri na siyasa. Zan zama matar tsohon shugaban ƙasa, me kuma nake nema?
” Ina shawartar matar shugaban kasar da zai gaji miji na da cewar Kar ta yi kwana-kwana, kuma kar ta bari wani ya zo ya mamaye gwamnatinsu. Su saurari mutanen da suka zaɓe su. Dole ne su saurari jama’a.