Labaran cinikayyar kasuwar yan kwallan kafa

Ana gab da ayyana Kolo Toure a matsayin sabon shugaban Wigan. Tsohon dan wasan kuma mai tsaron gida na kungiyoyin Manchester City, Liverpool da Ivory Coast mai shekara 41, a yanzu kociya ne a kungiyar Leicester. (Sun)

Leicester na sha’awar dauko dan wasan baya na Jamus Robin Gosens, mai shekara 28, wanda ke taka leda a Intermilan. (Calciomercato – in Italian)

Manyan kungiyoyin League ka iya dauko dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, daga Manchester United – a farashin fam miliyan 210m albarkacin kamfanin Talbijin na Apple da ke ciki tsundum . (iNews)

Bruno Fernandes ya ce ba bu wata jikakkiya tsakaninsa da dan wasan Portugal da Manchester United wato Cristiano Ronaldo duk da cewa an dauki bidiyo da hotunan ‘yan wasan biyu su na musayar yawu. (Sky Sports)

Tsohon shugaban Tottenham Mauricio Pochettino ya ce an kyankyasa masa dalilin da ya na shi zama shugaban kungiyar Manchester United, sai dai labarin ya je a kurarren lokaci, amma ya ce rai da rabo, watakil nan gaba ya samu wannan damar. (Radio Marca, via Mirror)

 

Barcelona za ta sai da dan wasan gaba na Netherlands Memphis Depay mai shekara 28 a watan Janairun badi. (AS – in Spanish)

Ejan din dan wasan gaba na Manchester United Uruguay Facundo Pellistri, mai shekaru 20, zai bar Old Trafford a watan Janairu mai zuwa, tun da har yanzu bai buga wani babban wasa a kulub din ba. (El Observador – in Spanish)

Dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid da Brazil Vinicius Junior, mai shekara 22, ya na fargaba kan raunin da ya ji gabannin fara gasar cin kofin duniya da ke tafe, saboda fargaba magautansa a La Liga. (ESPN)

Murna ta koma ciki ga masoya wasan kwallon kafa da suka tafi kallon gasar cin kofin duniya, da kungiyoyi masu zaman kansu suka dauki nauyinsu domin karfafa gwiwar ‘yan wasa, sakamakon soke alawus da aka shirya za a dinga ba su a kowacce rana (Guardian)

Tsohon dan wasan tsakiya na Arsenal da Chelsea Emmanuel Petit na hasashen Brazil ka iya lashe gasar cin kofin duniya da za a fara a Qatar. (Mirror)

Shi kuwa Darren Bent na hasashen, watakil manajan Ingila Gareth Southgate ya iya ajiye aiki, bayan kammala gasar cin kofin duniya, ko da kuwa kungiyar ta kai bantenta ko rashin nasara. ( Talksport)

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments