Shugaban kasar China Xi Jinping, ya bayyana kudurin sa na cewa, kasarsa ta shirya hada hannu da kasar New Zealand, wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da kwanciyar hankali, a kasashen dake tsibiran tekun Pasifik.
Shugaba Xi wanda ya bayyana haka yayin da yake ganawa da firaministar New Zealand, Jacinda Ardern a gefen taron shugabannin kungiyar APEC karo na 29, ya ce neman zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa, sun kasance mafarin manufar kasar Sin game da kasashen tsibiran tekun Pasifik.
A nata bangare, Jacinda Ardern, ta ce ya kamata kasashen biyu sun hada hannu wajen kara musaya da zurfafa hadin gwiwa a bangarorin cinikayya da tattalin arziki da ilimi da sauyin yanayi da sauran bangarori. Kuma New Zealand, na ganin Sin a matsayin babban karfi dake ingiza makomar ci gaba da zaman lafiyar duniya, tana mai cewa, kasarta ta aminta da manufar kasar Sin daya tak a duniya.
Har ila yau, a birnin Bangkok a yau Juma’a, shugaba Xi ya gana da Sarkin Brunei, Sultan Hassanal.