Gwamnatin Tarayya ta bayyana mayakan ISWAP da ke kai hare-hare a yankunan arewacin kasar a matsayin wandanda suka kai kazamin hari a Cocin Katolika dake Owo a Jihar Ondo wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 40.
Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka bayan taron majalisar tsaron kasa da ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Aregbesola yace gwamnati tayi nasarar gano wadanda suka kai kazamin harin ta’addanci, kuma ‘yayan wannan haramcaciyar kungiyar ce ta ISWAP wadda ta dade tana kashe mutane a arewacin Najeriya.
Ministan wanda ya gana da manema labarai tare da Sufeto Janar na Yan Sanda Alkali Usman Baba yace tuni aka baiwa hukumomin tsaron kasar umurnin farautar maharani domin ganin sun fuskanci hukunci.