watan Afrilun shekarar 2020, wani taro da Musulmai suka yi da ya janyo yaduwar cutar korona a Indiya, ya zamo sila na ƙaruwar ƙin jinin Musulunci.
Dubban masu wa’azi daga cikin kasar da ma waje ne suka halarci taron a Delhi, wanda wata kungiya mai suna Tablighi Jamaat ke shiryawa shekara da shekaru.
Jam’iyya mai mulki ta Narendra Modi BJP, ta kira taron a matsayin taron yaɗa cuta.
Masu ƙin jinin Musulmai da wasu kungiyoyi sun ɗora alhakin yaɗa cutar a kan taron, inda aka rinka yadawa a shafukan sada zumunta ana rubuta “A kare kasarmu daga annobar korona.”
Indiya dai ta tuhumi kusan mutum 1,000 da suka halarci taron da karya dokokin kullen korona.
Yawancin masu wa’azin da suka je taron daga Indonesiya suke, wato abokiyar huldar kasuwancin Indiya.
‘Yan majalisar dokokin kasar sun yi zargin cewa ana amfani da wannan taron ne wajen muzgunawa Musulmi a Indiya.
Wani jami’in diflomasiyya a Indiya ya ce wannan misali ne na irin rikicin cikin gidan da ke faruwa.
Irin abin da ke faruwa a Indiya a kan batun kalaman batanci ga Musulmi a yanzu ba shi ne na farko ba da jam’iyya mai mulki ke fuskantar suka akai ba.
Shekaru biyu da suka wuce, dan majalisa daga jam’iyyar BJP, Tejasvi Surya, ya fuskanci suka bayan da ya wallafa wani abu a shafinsa na tuwita a kan batun mata Larabawa.
Fitattun mutane da suka hada da ‘yan kasuwa da lauyoyi da ma masu sharhi a Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait, sun yi Allah-wadai da kalaman nasa, abin da ya sa daga baya ya koma shafin nasa ya goge.
Haka a shekarar 2018 ma, a wani taro da aka yi, ministan harkokin cikin gidan kasar Amit Shah ya yi wasu kalamai marasa daɗi ga ‘yan kasar Bangladesh da suka shiga Indiya ba bisa ka’ida ba.
Wannan kalamai sun harzuƙa al’ummar Bangladesh wadda ke da yawan Musulmai, ind ahar wani babban jami’i a kasar ya bayyana kalaman ministan a matsayin marassa tushe da amfani.
A cikin shekara ɗayar da ta wuce an sha samun ɓarin kalaman ƙiyayya ga al’ummar Musulmai da yawansu ya kai miliyan 200, daga bakunan shugabannin al’ummar addinin Hindu masu ra’ayin riƙau
Wasu daga cikinsu ma a bayyane suka dinga tunzura mabiya addinin Hindun da su ɗauki makamai su aiwatar da kisan kiyashi a kan Musulmai.
Ana dai yawan samun kalamai marasa dadi da ake yi wa Musulmai a Indiya, wasu ma a shafukan sada zumunta ake wallafa su.
Akwai lokacin da mata ‘yan jarida Musulmai suka fusata bayan da aka rinƙa sanya hotunan mata a shafukan sada zumunta wai ana tallata su.
Gwamnatin Mr Modi ba ta cika daukar mataki ba, sai dai ta yi shiru ko ta yi ta jan kafa wajen mayar da martani ko kuma ta ɗora alhakin hakan kan wasu da ba ta ambatar sunansu.
Duk irin wadannan abubuwan babu abin da suke yi in ban da ƙarfafawa mabiya addinin Hindu gwiwar ci gaba da cungunawa Musulmai da ɓata musu suna a shafukan sada zumunta.
Lokacin da Indiyawa mazauna Hadaddiyar Daular Larabawa suka fara sanya abubuwa da suka jiɓanci ‘yan kungiyar Tablighi Jamaat a 2020, wata babbar ‘yar kasuwa da ke da alaka da masauratar kasar ta wallafa a shafinta na tuwita cewa duk wani da zai rinka nuna wariya ta addini ko kabilanci to za a ci shi tara sannan kuma zai bar kasar.
A wannan karon ma kalaman batancin da ‘yar majalisar Indiya ta yi ya janyo suka daga kasashe 15 ciki har da Saudiyya da Iran da kuma Qatar.
Wannan dalili ala dole ya sa Mr Modi ya dakatar da mai magana da yawun nasa da ta yi kalaman.
Yawancin shugabannin jam’iyyar BJP sun yi amanna cewa duk ɗaga jijiyoyin wuyan da ake yi ba da jimawa ba komai zai daidaita.
Gaba daya dai, akwai daɗaɗɗiyar alaƙa mai ƙarfi tsakanin India da kasashen yankin Gulf.
Akwai Indiyawa kusan miliyan 8.5 da ke aiki a kasashen yankin Gulf, inda suka ruɓanya ‘yan Pakistan.
Haka kuma akwai Indiyawa da dama a yawancin kasashen duniya.
Kuma irin wadannan Indiyawa da ke aiki a kasashe na aikewa da kudi kamar dala biliyan 35 gida a kowacce shekara inda suke tallafawa iyalansu da za su iya kai wa miliyan 40.
Huldar kasuwanci tsakanin Indiya da kasashen yankin Gulf ta kai ta dala biliyan 87.
Iraƙi ce ta fi shigarwa da Indiya man fetur, sai Saudiyya.
Fiye da kashi 40 cikin 100 na iskar gas din Indiya na zuwa ne daga Qatar, wannan ne dalilin da ya sa Firaministan ke bai wa kasashen yankin Gulf din muhimmanci.
A wannan karon gwamnatin Mista Modi da ƙwararru ba su mayar da martani da wuri ba.
“Akwai alamun cewa idan irin wadannan abubuwan suka faru, to tabbas za su zo da ƙalubale.
Dole ne gwamnati ta san abin yi. Shin tana son ta shiga cikin ruɗu da ruɗani ne?” a cewar Farfesa Raghavan.