Daga Walid Hari.
Tawagar alkalan ta mutum uku da Mai Shari’a Jummai Hanatu ta jagoranta ta ce Kanu ba shi da laifin amsawa saboda tun farko Babbar Kotu ba ta da hurumin yi masa shari’a tun farko.
Hukuncin kotun ya ce matakin kamo Kanu da aka yi da dawo da shi Najeriya daga Kenya ya kauce wa doka.
Kotu ta ƙara da cewa shirun da gwamnatin ta yi na nuna cewa ta yarda da abin da Kanu ya ce cewa sato shi aka yi aka dawo da shi Najeriya da ƙarfi.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, lauyan Kanu kuma ɗan rajin kare hakkin ɗan adam, Ifeanyi Ejiofor, ya rubuta a shafinsa Facebook a ranar Alhamis cewa, “a ƙarshe dai Kanu ya yi nasara.
“An ba da damar ɗaukaka ƙara, an saki tare da wanke Oyendu Mazi Nnamdi KANU. Mun yi nasara!, ya rubuta.