Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Hukamar Hisbah ta jihar Kano ta dauki gabarar shigewa gaba wajan gudanar da auren wani Ba zawarcin mai suna, malam Surajo Ibrahim kurnar Asabe da bazawara, malama Yahanasu da suka bukaci, Babban Kwamandan Hisbah ya zama wali kuma ya tallafa ta yadda auren zai sami dukkan tagomashi da inganci, irin na sauran ma’aurata.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Lawan Ibrahim Fagge, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa.
Tun da fari, bazawara malama Yahanasu ta shiga kafar yada labarai ta yi tallar kan ta cewar ta ga ji da zaman gwauranta.
kuma kasancewar a baya ta taba yin aure kuma a wannacan auren ta haifi yara uku sai auren ya mutu, tun daga wannan lokaci, babban burinta ta sami Wanda za su yi aure kuma ya rike ta har da ya yanta gabaki daya ba tare da nuna wa ya ya kyara ko tsangwamaba.
Jin wannan tallar da bazawara malama Yahanasu ta yi sai ya zo dai da bukatar bazawari malam Suraja Ibrahim kurna kuma ya ce ya ji ya gani yana so.
ko da malam Surajo Ibrahim ya yi to zali da bazawara malama Yahanasu wacce ta yi tallan kan ta a kafar yada labarai sai ya ce tayi dai dai da kalar matar da ya ke so.
Daga bisani su ka garzayo hukumar Hisbah ta jihar Kano domin hukumar ta shigo ta fuska biyu fuskar farko shine da ta bincike ma’auranta kamar yadda shari’ar musulinci ta shimfida fiska na biyu kuma ta tallafawa auren kan sa, ta yadda hukumar Hisbah za ta zama a tsakgai tare dauka gabaren yin daurin aure da sauran hidimar kamar yadda a ke auren zawarawa a shekarun baya