Daga Dantala Uba Nuhu Kura
Tuni kotu ta tasa keyar wasu matasa Biyu Da Ake Zargin Daya da sata daya kuma da sayan kayan satar zuwa gidan maza.
Matasan  daya Mai Suna Sunusi Rabiu Ciromawa kotun tana tuhumar sa da laifin Haura Katanga tare da Satar Injin Buga Ruwan leda wanda akafi Sani da table water Mai Kimar Kudi Naira Milliyan Daya Da Dubu Dari shida 1,600,000.
  Dayan kuma mai suna Sunusi Sani Mutumin Danbatta kotun tana tuhumar sa ne da laifin Sayan kayan sata.
    Matasan dai tuni Idonuwansu suka Raina Fata Yayin Da Suka Fada komar Jamian Tsaro na Karamar Hukumar Garun-Malam inda daga bisani aka Gurfanar Dasu a Gaban Kotun Shariar Musulunci ta Karamar Hukumar Kura wadda Maisharia Malam Ibrahim Isa Usman yake jagoranta.
    Bayan Maigabatar Da Kara Insifecta Maaji Ya Karantawa Mai Lefi Na Farko Sunusi Rabiu kunshin tuhumar da ake masa a take ya amsa laifin sa
Sannan mai laifi na biyu da ake Tuhuma da Sayen kayan sata Cikin Araha Sunusi Sani Danbatta wanda shima take ya amsa laifin sa.
Bayan kammala sauraron ne mai sharia Malam Ibrahim Isa Usman Ya dage Shariar Zuwa ranar 12-10-2022.