Obindo wanda ke jagorancin Tsangayar kula da masu fama da tabin hankali, a Cibiyar horar da likitoci ta Afirka ta Yamma dake Najeriya, ya bayyana cewar halin kula da masu fama da cutar tabin hankali a Najeriya ya tabarbare, ganin yadda alkaluma suka nuna cewar kasar na dauke da mutane sama da miliyan 60 dake fama da matsalar.
Masanin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewar, abin takaici shine kashi 90 na wadannan mutane dake fama da matsalar basu da hanyar zuwa asibiti domin samun kula daga likitoci, sai kashi 10 kacal wadanda basu da yawa.
Daga cikin matsalolin da masanin ya gabatar a matsayin wadanda ke hana masu fama da cutar samun magani, sun hada da rashin bayani dangane da abinda ke haifar da cutar da kuma yadda ake kula da ita, da kuma yadda hukumomin Najeriya ke yiwa matsalar rikon ko-in-kula da kuma al’adar wasu ‘yan Najeriya dangane da matsalar, sai kuma karancin kwararrun likitocin dake kula da masu fama da cutar.
Obindo ya kuma bayyana karancin asibotocin da ake kula da masu fama da cutar, ganin cewar akasarin jihohin da suke da su, sun sanya su ne a birane, yayin da sama da kasha 60 na jama’ar Najeriya ke zama a yankunan karkara.
Masanin ya bukaci sake fasalin kula da lafiyar ‘yan Najeriya domin sanya shirin kula da masu fama da tabin hankali a cikin ayyukan kananan asibitocin dake yankunan karkara.