SINGA MARKET.
Shugabancin kungiyar kasuwar Singa ya bukaci Gwamnati ta tallafawa mata da suke gudanar da kasuwancinsu a kasuwar domin habaka kasuwancinsu da ci gaban tattalin arzikin jihar Kano.
Shugaban kula da al,amuran mata ta kungiyar kasuwar, hajiya Maryam Musa Gawuna ce,ta bukaci haka a wata tattaunawa da manema labarai a kasuwar ta Singa.
Maryam Gawuna ta ce,tallafawa mata da jari a kasuwanci yana da mutukar mahimmanci a halin yanzu da al,amura suka lalace,Wanda kasuwanci ya tsinci kansa a cikin,kuma yana bukatar masu Ruwa da tsaki a fannin harkokin kasuwanci su kawo masa daukin gaggawa.
Shugabar ta yi kira ga Gwamnatoci a matakai daban_daban, da su ci gaba da tallafawa mata da jari domin rage masu zaman kashe Wando da yawaitar talauci tsakanin al,umma,musamman mata.
Hajiya Maryam Gawuna, ta kuma,yi kira ga mata da su daina raina kananan sana,oi duba da cewa daga karamar sana,a ne, ake samun bunkasa ta zamo Babba tare da tallafawa wasu da dama, inda tace,yanzu lokaci ya canza an daina raina kananan sana,oi kasancewar da kanana ne ake samun habaka zuwa Babba.
Haka zalika,tace,mata suna da rawar takawa a fannin harkokin kasuwanci da bunkasar tattalin arziki a kasar nan, shi ya sa kamata ya yi Gwamnatocin jihohi Dana tarayya a matakai daban daban su yi duk mai yiyuwa domin ganin sun tallafawa mata da jarin da za su rike Kansu da iyalansu,kasancewar an samu sauyin rayuwa da al,amura sun yi tsamari,musamman yadda ake samun hauhawar farashin kayayyakin masarufi a fadin kasar nan da alumma suke fama da matsin halin rayuwa.
Daga karshe ta yi kira ga yankasuwa da masu hannu da shuni akan su rika saukakawa a kayayyakinsu da zarar, sun samesu a cikin sauki domin alumma su ji dadin gudanar da rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana.
Maryam Gawuna, ta jaddada kudirinta na ci gaba da kiraye_kiraye ga shugabanni da yansiyasa a matakai daban daban ,wajan ganin an tallafawa mata a koina suke a fadin kasar nan, kasancewar a kashi Dari,kaso tamanin mata ne suke tsayawa domin zabar shugabannin kasar nan.
/COV/Ibrahim Sani gama/