A yammacin wannan rana ne ta lahadi daukacin tsaffin daliban da suka kammala makarantar rimi city primary school a shekara 2006 suka gudanar da taron da suka saba gudanarwa a duk shekara taron ya samu halartar tsaffin daliban da dama.
Daga wakilin aksammedia
A yayin taron mun samu ikon zantawa da shugaban wannan kungiyar ta dalibai tijjani bala isa wanda akafi sani da nani ya bayyanawa majiyar mu cewar sunyi duba da irin halin ko in kula da yawa yawan tsaffin dalibai suke yi
Shugaban ya bayyana irin gudummawar da suka kawo wa wannan makaranta na kayan kula da lafiya na taimakon farko tare da yiwa allunan da basu da fenti fenti
Shugaban SBMC na wannan makaranta Alhaji gambo madaki yakasai ya yaba da irin wannan aiki na wannan kungiyar ta tsaffin dalibai da daya taretamkar da dubu da addu’ar sanya san albarka da fatan alkhairi ya kuma bayyana cewar wadannan dalibai sun ciri tuta na ganin ba wata hadakar kungiya datake taimakawa wannan makaranta
Ya bayyana cewar bawai ba a taimakawa wannan makaranata ba irin taimakon hadaka ne ba a samu amma dai daikiu suna yiwa wannan makaranta hidima