Daga Walid Hari.
Kocin Newcastle United Eddie Howe ya ce ba zai dauko Cristiano Ronaldo, dan wasan gaba na Manchester United da kasar Portugal ba saboda shekarunsa na haihuwa da suka zarta 37. (90min)
AC Milan na iya dauko Ruben Loftus-Cheek, dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila mai shekara 26 a watan Janairu mai zuwa. (Calciomercato – in Italian)
Akwai kuma rahoton da ke cewa Chelsea na shirin tsawaita zaman Reece James, dan wasanta na baya mai shekara 22 da Mason Mount, dan wasanta na tsakiya mai shekara 23 a kungiyar, tun gabanin Ba’Amurke Todd Boehly ya saye kungiyar a watan Mayu. (CBS Sports)
Kocin Ingila Gareth Southgate na iya karbar alawus din fam miliyan 4 idan har ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta kasar wato Three Lions ta sami nasarar lashe kofin duniya a Qatar. (Sun)
Manchester City ba za ta fuskanci wata matsala ba wajen daukar Kylian Mbappe mai shekara 23, wanda ke son barin Paris St-Germain duk da cewa ya sabunta kwantiraginsa.