A baya bayan nan, Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya, ya bayyana fatan kasar Saudiyya na shiga kungiyar kasashe biyar masu manufar bunkasa tattalin arzikin su dana Duniya wato BRICS.
Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce a matsayin kasar China na jagorar kungiyar BRICS a bana, kasar za ta tallafawa kasashen kungiyar wajen aza harsashin su na fadada yawan mambobin kungiyar, da kara inganta hadin gwiwar kasashen kungiyar.
Wang Wenbin, ya ce bayan shekaru 16 ana raya hadin gwiwar kungiyar BRICS yanzu haka an Sami manyan nasarori, tare da samar da muhimmiyar gudummawa a fannin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya.
A cewar sa hakan, salo ne na gudanarwar BRICS da ya samu yabo da goyon bayan sassan kasa da kasa.
Kazalika, karin kasashen duniya na fatan zama mambobin kungiyar ta BRICS, domin yin aiki tare, don shawo kan wahalhalu da kalubale, tare da cimma moriyar bai daya da wadata.