Yan bangar siyasa sun lakaɗa wa shugaban ƴan jaridu na Jihar Zamfara duka
Ƴan ɓangar siyasa sun lakawada shugaban ‘yan jarida na Jihar Zamfara, Comrade Ibrahim Musa Maizare duka, inda kuma suka yi barazana ga ‘yan jaridu a fadin jihar. ƴan bangar dai sun yi dirar mikiya a ofishin shugaban ƴan jaridun, inda su ka umurci ma’aikata da ke aikin gyara wasu shaguna na kungiyar a sakatariyarta na jiha da su daina aikin gyara shagon wanda ake son amayar da shi a matsayin ofishin yaƙin neman zaɓe.
Ɓata garin sun ce ɓa za su bar wajen ba saboda wani dan siyasa ne basu, kuma muddin yana raye ba za su bar wurin ba.
Tun da farko an karɓi hayar shagon ne domin ɓude wajen sayar da abinci, sai dai, bayan wanda suka kama shagon sun tashi, ƴan banga su ka mayar da shi zuwa ofishin ƴakin neman zaɓe jam’iyyar su, inda a 2021, wasu ƴan banga na daban suka ƙona shagon.
Duk da zuwan jami’an tsaro sakatariyar ƴan jaridun, ƴan bangar sun ci gaba da zage-zage kan shugabanni da kuma sauran mambobin ƙungiƴar ‘yan jaridun na jihar Zamfara.
Da yake magana jim kadan bayan faruwar lamarin, Sakataren kungiyar, Ibrahim Ahmad Gada, ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbata sun kare rayuka da ma dukiyoyin ‘yan jarida a jihar saboda rayuwarsu na cikin barazana a yanzu.