Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa tabbas ƙasarsa ta girke makaman nukiliya a Belarus.
Lokacin da yake bayani a wurin taro kan tattalin arziƙi, Putin ya ce za a yi amfani da makaman ne kawai idan aka yi barazana ga iyakokin Rasha.
Sai dai Amurka ta ce babu wata alama da ta nuna cewa Rasha na shirin amfani da makaman nukiliya wajen kai wa Ukraine hari.
“Ba mu ga alamar cewa Rasha na shirin amfani da makaman nukiliya a kan Ukraine ba.” In ji sakataren harkokin waje na Amurka, Antony Blinken.
Belarus na daga cikin manyan ƙawayen Rasha, kuma Rasha ɗin ta yi amfani da ita a matsayin sansani gabanin ƙaddamar da samame kan Ukraine a bara.
Nau’in makaman nukiliyan da Rashar ta jibge a Belarus su ne marasa ƙarfi a cikin makaman nukiliya da ke jibge rumbun makamanta.
Lokacin da yake amsa tambayoyi bayan kammala jawabi a taron tattalin arziƙi na duniya a birnin St Petersburg, Putin ya ce lamarin wani “mataki ne da zai tunatar da duk wanda ke shirin cutar da Rasha.”
Lokacin da aka tambaye shi game da batun amfani da makaman, Putin ya ce: “Me zai sa mu sanya duniya cikin barazana? Na riga na faɗi cewar za a yi amfani da irin wannan ƙarfi ne idan muka ga akwai barazanar Rasha za ta faɗa cikin hatsari.”
Mista Putin ya kuma sake nanata iƙirarinsa na cewa Ukraine ba za ta taɓa cin nasara ba a yunƙurinta na kai wa Rasha hari.
Ya ce nan da lokaci ƙalilan makaman Ukraine za su ƙare, inda za ta koma dogaro da waɗanda ƙawayenta ke ba ta gudunmawa.
Kuma a cewarsa wannan ba abu ne mai ɗorewa ba.