Matakin na zuwa ne sakamakon janye wasu ayyukan tallafawa ‘yan cirani da kasashen suka yi bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.
Hukumomin da ke kula da ‘yan cirani da kasar Algéria ta koro sun bayyana damuwa bayan da kungiyoyin agaji suka dakatar da tallafin da suke bai wa hukumomin domin gudanar da daukar nauyinsu.
‘Yan ci rani da kasar Algeria ta koro da suka je kasar domin samun abinci sun samu kansu a cikin tsaka mai wuya bayan da kungiyar tarayyar Turai ta dakatar da tallafin da take bai wa Nijar sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli.
Hakan na faruwa ne sakamakon yadda kasar Algeria ke ci gaba da koro ‘yan Nijar daga kasar.
A baya sai da kasar ta koro wasu yara ‘yan kasar Nijar akalla fiye da 60 da suka je kasar ta Algeria ci rani, abin da ake ganin zai dagula al’amurra na daukar nauyin ‘yan ciranin.
Isma’il Toufa Ibrahim wani jami’i a ma’aikatar da ke kula da kananan yara ya ce tuni dai sojojin da suka yi juyin mulkin suka kira kungiyoyin agaji da ke zaune a Nijar da su dauki nauyin ‘yan kasar Nijar.
A nasu bangare kungiyoyin agajin irin hukumar da ke kula da bakin haure cewa suka yi sun yi na’am da bukatar da hukumomin suka gabatar musu na daukar nauyin ‘yan ci ranin Nijar da kasar Algeria ta koro a cewar Mahaman wani jami’i a hukumar da ke kula da bakin haure.