Babban mashawarci game da kiwon lafiya na kasar China Liang Wannian, ya ce “manufar ganowa da kuma kawar da cutar COVID-19 nan take” da kasar Sin ke aiwatarwa, ta yi kyakkyawan tasiri wajen dakile yaduwar cutar cikin sauri a kasar.
Liang ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, yayin taron manema labarai da ya gudana. Yana mai cewa, makasudin aiwatar da tsarin shi ne hana yaduwar cutar tsakanin kananan rukunonin al’umma, ta yadda za a kai ga dakile fantsamar ta cikin al’umma baki daya.
Babban masanin ya kara da cewa, baya ga dan sauyin kariyar garkuwar jiki da aka samu, Sinawa ba su samu cikakkiyar kariyar ainihi ta garkuwar jiki daga cutar ba, saboda manufar da ake aiwatarwa.
Ya ce idan har aka sassauta “manufar ganowa da kawar da cutar COVID-19 nan take”, hakan zai haifar da gagarumar bazuwar cutar, wanda zai sabbaba mutuwar tsofaffi da masu cututtuka dake da tsanani.
Liang ya ce Sin ba za ta bari a samu yawaitar bazuwar wannan annoba ba, da mace-macen al’umma, don haka ya zama wajibi a zage damtse wajen kare lafiyar al’umma.
A daya hannun kuma, masanin ya ce akwai batun rashin tabbas don gane da tasirin cutar cikin dogon lokaci, ko batun yiwuwar sauya halittar kwayoyinta, don haka manufar Sin Kenan na ganowa da kuma kawar da cutar COVID-19, wadda a yanzu ake ganin tasirin ta, ita ce hanya mafi dacewa ta kaucewa yanayin rashin tabbas game da cutar