A matsayin wani mataki na mayar da martani, gwamnatin kasar Sin ta kakabawa wasu Amurkawa su biyu takunkumi, biyowa bayan takunkumin da gwamnatin Amurka ta kakakawa wasu jami’an kasar Sin su biyu a ranar 9 ga watan nan na Disamba, sakamakon zargin da Amurkan ta yi musu, wai masu alaka da wasu batutuwa masu nasaba da hakkin bil adama a Tibet.
A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, karkashin tanajin dokar mayar da martani ga matakan takunkumi daga sassan ketare ta kasar Sin, bangaren Sin din ya yanke shawarar ramawa-kura-aniyarta, ta hanyar kakabawa Miles Maochun Yu, da Todd Stein takunkumi.
Takunkumin ya shafi daskaras da dukkanin kadarorin su dake kasar Sin. Kaza lika an haramtawa duk wata hukuma, ko daidaikun mutane dake kasar Sin yin duk wata mu’amala da mutanen biyu. Har ila yau, an haramta musu, da dukkanin iyalan su samun bizar shiga kasar Sin, kuma dukkanin matakan da aka dauka a kan su, za su fara aiki ne tun daga Juma’ar nan. (