Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ya ce adadin yara dake fuskantar mummunan tasirin fari a kasashen Habasha, da Kenya, da Somaliya, ya ninka cikin watanni 5 da suka gabata.
Alkaluman asusun na UNICEF, sun nuna yadda yara kimanin miliyan 20.2, daga wadannan kasashe 3 ke fama da barazanar yunwa, da kishirwa da cututtuka, adadin da ya haura yara miliyan 10 da aka samu a watan Yuli, lamarin da ake alakantawa da tasirin sauyin yanayi, da hauhawar farashin kayayyaki, da karancin hatsi dake addabar yankin na kahon Afirka.
UNICEF ya ce kusan yara miliyan 2 a kasashen 3, na fama da matsananciyar bukatar tallafin jin kai, a fannin shawo kan kamfar abinci mai gina jiki, wanda yanayi ne mai hadari a fannin wadatar abinci.
Kari kan hakan, alkaluman na UNICEF sun nuna cewa, akwai kusan yara miliyan 2.7 da ba sa zuwa makaranta saboda kalubalen fari, yayin da karin yaran kusan miliyan 4 ke fuskantar yiwuwar ajiye karatu.
UNICEF ta yi gargadin cewa, iyalai da dama na fuskantar matukar matsin rayuwa, yayin da yara ke tunkarar matsaloli masu alaka da tilasa musu yin ayyukan karfi da auren wuri.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, mataimakiyar daraktan shiyyar gabashi da kudancin Afirka ta asusun UNICEF Lieke van de Wiel, ta ce akwai bukatar samun gudummawar dukkanin sassan kasa da kasa, wajen samar da albarkatu da gaggawa, domin rage fadadar mummunan tasiri, a rayuwar yaran dake wannan yanki na Afirka