Karon farko China ta harba kumbo izuwa Duniyar Rana domin wani bincike

Sashen binciken ilimin taurari na cibiyar nazarin kimiyya ta Kasar Sin, ya ce a karo na farko, kasar ta harba kumbon binciken duniyar rana.

An harba kumbon ne a jiya Lahadi, bisa amfani da rokar Long March-2D, daga cibiyar harba tauraron dan Adam na Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar da misalin karfe 7:43 agogon Beijing.

A cewar Gan Weiqun, babban masanin kimiyya na cibiyar nazarin ilimin taurari na Purple Mountain Observatory dake karkashin cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin, wannan ne kumbo na farko da zai yi binciken yanayin fitar maganadisu da makamashi na duniyar rana, a lokaci guda.

Kumbon ya kunshi kirkire-kirkire da dama kamar na’urar bibiyar yanayin rana da aka sanya masa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments