ChatGPT wata manhaja da ke iya kwaikwayon tattaunawar mutane wacce Kamfanin OpenAI ya kirkira zata iya ba da gamsassun amsoshi akan batutuwa da yawa a matsayin manhaja da ke mu’amala da mutane ta hanyar tattaunawa. Saboda yadda take kwaikwayon dabi’un mutane akwai wadanda ke sa ta rubuta waka, da masu son ta rubuta kundin sakonni na na’urori wato coding…
ChatGPT manhaja ce ta harshe wacce aka horar da ita ta hanyar amfani da na’urori masu kwakwalwa wadanda ke kwaikwayon dabi’un mutane.
Kamfanin bincike kan na’urori masu kwakwalwa da ke kwaikwayon dabi’un mutane na OpenAI ne ya samar da ita ga duk duniya a ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2022 kuma manhajar ta samu masu amfani da ita miliyan daya cikin kwanaki biyar kacal. A cikin tattaunawar da masu amfani da ChatGPT, ana ganin cewa manhajar na iya samar da amsoshi masu ma’ana da gamsarwa akan batutuwa da yawa.
An horar da manhajar, wacce ke iya samar da amsoshi irin na mutum, da manyan bayanan rubutu daga yanar gizo, kuma an ce zata iya maye gurbin injunan bincike a cikin shekaru masu zuwa.
ChatGPT na amfani da fasahar GPT-3, wacce aka bayyana a matsayin daya daga cikin fasahohin sarrafa harshe mafi girma kuma mafi karfi har zuwa yau. Abun da ke banbanta ChatGPT shi ne cewa an inganta ta don “tattaunawa.”
Devrim Danyal, wanda ya kafa Kwalejin Fasaha, ya jaddada cewa ChatGPT na aiki ne ta hanyar amfani da ra’ayoyin masu amfani.
Yana da wahala a fadi abun da ChatGPT zata iya yi. A misali, tana iya rubuta makala kan kowane batun da ake so, shirya kyakkyawan tsari na aiki, har ma ta rubuta wakoki, labarai, wasan kwaikwayo da yadda ake girke-girke…
ChatGPT har yanzu tana da iyaka kuma Kamfanin OpenAI yana jaddada cewa har yanzu manhajar na matakin gwaji. Tun da yake an horar da wannan manhajar tare da manyan bayanan rubutu daga yanar gizo, ya kamata a san cewa bayanan da take bayarwa na bukatar tabbaci.
Devrim Danyal, wanda ya kafa Kwalejin Fasaha, yana tunanin cewa manhajar zata iya canzawa zuwa tsarin yanke shawara idan ta samar da bayanan da ba sai an tabbatar da su ba a nan gaba.