Daga Hadiza Muhammad Mai Taya
Sama da Musulmai miliyan dubu ɗaya ne suka fara azumi a faɗin duniya a wannan makon, inda za su shafe tsawon wata guda suna azumin na watan Ramadana.
Azumin wanda ake fara shi daga lokacin sahur a sauke shi bayan faɗuwar rana ana yin shi ne na tsawon sa’a 12 zuwa 18 a ko ina a faɗin duniya, amma hakan ya danganta da wanne saƙo mutum yake zaune a duniya.
Musulmai da dama a duniya sun yi amannar azumin Ramadana na ɗaya daga cikin ginshiƙan abubuwa biyar da addinin Musulunci ya kafu a kansu, tun lokacin Annabi Muhammad (SAW)sama da shekara 1,400 da suka gabata.
Lokacin azumi ana nesantar cin abinci da sha da duk wani abu mai alaƙa da saduwa tsakanin namiji da mace daga lokacin da aka yi sahur har zuwa faɗuwar rana.
Akan samun raguwar kwanaki 10 zuwa 14 a kowacce shekara idan aka kwatanta da lokacin da aka fara azumin a shekarar da ta gabata.
Hakan ya samu asali ne kan yadda jadawalin watannin Musulunci ke da watannin da suke ƙarewa ne tsakanin kwana 29 zuwa 30.
Duka watannin babu mai kwana 28 kamar watan Fabarairu a jadawalin watannin shekarar Miladiyya, ko kuma mai kwana 31 kamar watan Disamba.
A wannan shekarar an fara azumin ne a ƙasashe irin su Saudiyya da Najeriya a ranar Alhamis 23 ga watan Maris.
Saboda jadawalin shekarar Hijira ya gaza ta Miladiyya da kwana 11, wanda hakan ya sa za a yi azumin watan Ramadana sau biyu a 2030 – za a fara na farko a ran 5 ga watan Janairu na biyu kuma a ranar 25 ga watan Disamba.
Ƙasashen da za a yi azumi mafi gajarta a 2023
A wannan shekarar Musulman da ke ƙasar Chile ne za su yi azumi mafi gajarta, domin za su azumci watan Ramadana na tsawon sa’a 11 da rabi a kullum.
Idan mutum na zaune a kudancin duniya wajen su New Zealand da Argentina da kuma Afrika ta Kudu, suma za su yi azumi maras tsayi na sa’a 11 zuwa 12 a watan na Ramadana.
Musulmin birnin Reykjavík da ke Iceland, azuminsu zai zama cikin mafiya tsayi a bana.
Ana sa ran za su yi azumi sa’a 16 da minti 50 a kowacce rana cikin wannan wata mai tsarki.
Najeriya: randa za su yi mara tsari – sa’a 13 da minti 18, mafi tsayi – sa’a 13 da minti 25
Tunisia: randa za su yi mara tsayi – sa’a 13 da minti 44, mai tsayi – sa’a 14 da minti 55
Morocco: mara tsayi – sa’a 13 da minti 37, mafi tsayi – sa’a 14 da minti 41
Egypt: mara tsayi – sa’a da minti 39, mafi tsayi – sa’a 14 da minti 34
Saudi Arabia: mara tsayi – sa’a13 da minti 29, mafi tsayi – sa’a 14 da minti11
Qatar: mara tsayi – sa’a 13 da minti 29, mafi tsayi – sa’a 14 da minti 13
Somalia: mara tsayi – sa’a 13 da minti 22 mafi tsayi – sa’a 13 da minti 27