Jam’iyar NNPP tabin sahun jam’iyu uku wajen neman a soke zaben shugaban kasa

Jam’iyyar NNPP da Sanata  Rabi’u Musa Kwankwaso ya yiwa takarar shugaban kasa,  ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta  ta kasa INEC da ta soke zaben shugaban kasa da take kokarin bayyanawa
Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali ne ya bukaci  hakan Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.
Sanarwa tace akwai kura-kurai Masu yawa da aka tabka a yayin zaɓen shugaban kasar da aka gudanar a ranar asabar 25 ga watan fabarairun shekara ta 2023.
Farfesa alkali ya ce a matsalolin da aka fuskanta akwai siyan kuri’u, rashin aiki da na’urar VBas a wasu sassa na kasa da hatsaniya a wasu wuraren sai rashin sanya sakamakon zaben mazabu a shafin tattara sakamakon zabe na INEC.
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments