Gwannatin tarayya ta kara adadin yawan sojoji a jihohin Zamfara Katsina da Sokoto wanda ake alakanta jibge jami’ai da kokarin kaucewa irin matsalar fasa gidan yarin da aka fuskanta a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Shaidun gani da ido sun ruwaito yadda jami’an tsaron da aka jibge ke rike da manyan makamai kuma suna ci gaba da sintiri a yankunan gidajen yarin jihohin uku.
Lamarin na zuwa ne kwanaki 11 bayan da jaridar Premium Times ta ruwaito rahoton gargadin da ke bayyana yiwuwar Kai harin ta’addanci a wasu gurare.
A jihar Katsina kakakin gidan yarin jihar Najib Idris ya tabbatarwa jaridar ta Premium Times cewa matakin jibge jami’an tsaron na da nufin bayar da kariya a gidan yarin don kaucewa harin ta’addancin.
Ba kadai a kewayen gidan yarin ba, hatta a tsakar jihar Katsina an ga karuwar zirga-zirgar jami’an tsaro a yankunan da suka kunshi Unguwar Yari da Kofar Soro da kuma sabon gidan yarin da ke kan titin zuwa Jibia duk da kasancewarsa gab da barikin Soji.
A jihar Kebbi rahotanni sun ce haka abin ya ke ta yadda jami’an tsaro suka yi dandazo a yankin Illelar Yari yayinda ake tsananta bincike kan duk masu shige da fice a anguwar.
Haka zalika jihar Zamfara inda al’ummar yankin Unguwaer Gwaza da ke Gusau ke ganin karuwar zirga-zirgar jami’an tsaro baya ga was una daban da aka jibge a kofar gidan yarin da ke wajen