Anyi kira ga gwamnatin tarayya kan ta yi duk maiyiwuwa wajen ganin ta daidaita farashin kayayyakin masarufi a fadin kasarnan domin alummarta su samu saukin rayuwar yau da kullun.
Shugaban kungiyar masu akori kura na kasa reshen railway da Masallacin jumaa na Fagge dake kano Alhaji Abubakar Dan Iya Bala ne ya yi wannan kiran a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Dan Iya Bala ya bayyana cewar sakamakon hauhawar farashin man fetur da Dizel a kasarnan Ya sanya farashin Kayayyakin masarufi ya tashi, kuma rayuwa tayi tsada, don haka yake kira ga gwamnati kan ta shiga lamarin wajen daitata farashin kayayyaki .
Shugaban ya kuma koka dangane da yadda Shugabancin kungiyar su a kullum yake hakurkutar da masu mota kan daure Kar su twawwala wajen yin cinikin daukowa dakai kaya zuwa sassa daban daban na kasarnan. Kazalika Ya bayyana cewar yanzu haka sakamakon hauhawar farashin man fetur da Dizel din ya sanya kowa ma kara farashin kayayyakin sa yakeyi yadda yaga dama, Don haka ya ke kira ga gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi umar Ganguje khadimul Islam ta saukaka alummar jiharnan ta hanyar Samar musu da walwala ta yadda zai rage musu radadin rayuwa. Daganan sai yayi kira ga yayan kungiyarsu dama sauran alummar jiharnan kan su tabbata sun mallaki katin zabe kasancewar dashi ne kadai Zasu iya sauya gwamnati ta hanyar zaben shugabanni nagari afadin kasarnan.
Daga karshe Sai ya yabawa yayan kungiyarsu bisa hadin kai da goyon baya dari bisa dari da suke baiwa Shugabancin kungiyar tare da kara basu hakuri dangane halin da kasarnan ke ciki tsadar rayuwa.