Kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na Borna ya tabbatar, yace karuwar adadin na zuwa ne a dai dai lokacin da ake samun karuwar masu shiga zanga-zangar kin jinin hijabi a karin birane da dama na kasar Iran
Kwana na takwas kenan ana ganin kakkarfar zanga-zangar a manyan biranen Iran ciki har da Tehran don nuna kyamarsu ga takurar da ake musu wajen tilasta su sanya hijabi ba da ra’ayinsu ba.
Tun farko dai zanga-zangar ta samo asali daga kamen Mahsa Amini ‘yar shekaru 22 da jami’an ‘yan sandan tabbatar da bin dokokin addini suka kama amma kuma kwanaki 3 bayan kamen suka sanar da mutuwarta, lamarin da ya sanya zargin ko su suka kashe ta .
Adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar Iran ya karu zuwa mutum 50, cikin mako guda da faro boren bayan kisan matashiya Mahsa Amini da ake zargin jami’an ‘yan sandan tabbatar da bin doka da aikatawa.