Babbar kotun tarayya dake zamanta a Jihar Legas ta yanke wa wani jami’in dan sanda mai suna Olalekan Ogunyemi hukuncin daurin rai da rai.
Mai shari’a Adenike Coker ta yanke hukunci ne ga Ogunyemi bayan samunsa da laifin bindige wani mutum da ya zo kallon kwallon kafa.
Yayin shari’ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu guda bakwai yayin da wanda aka yi kara ya gabatar da shaidu biyu
Ogunyemi, wanda ke aiki tare da tawagar yaki da yan kungiyar asiri na yan sanda, ya bindige Johnson a cikinsu a ranar 31 ga watan Maris na 2019 a wurin kallon kwallo a filin Mangoro, dake Ikeja, a jihar Legas.